Iyalai da abokan arzikin marigayin sun shiga jerin wakilan gwamnati, tare da baki daga kasashen waje, domin gudanar da addu'o'i na musaman ga shugaba Sata, taron da ya gudana ne a jiya Talata.
Yayin taron na jiya shugaban rikon kwaryar kasar ta Zambiya Guy Scott, ya bayyana cewa aikin da ya sanya gaba shi ne, tabbatar da nasarar zaben shugabancin kasar cikin nasara.
Marigayi shugaba Sata dai ya rasu ne yana da shekaru 77 a duniya, a wani asibiti dake birnin Landan. A yanzu haka kuma gwamnatin kasar ta ware makwanni 2, domin baiwa al'ummar kasar damar zaman makokin shugaban kasar.(Saminu Alhassan)