in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na Zambia
2014-06-19 15:01:41 cri
A ranar 18 ga wata a birnin Lusaka, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Zambia kuma mataimakin shugaban jam'iyyar PF, mista Guy Scott.

A yayin shawarwarin, Li Yuanchao ya bayyana cewa, ya kai wannan ziyara a kasar Zambia ne a daidai lokacin cika shekaru 50 da kasar Zambia ta samu 'yancin kai da kuma kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Zambia, kuma burin da yake neman cimmawa shi ne kara fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu a fannin siyasa, da inganta hadin gwiwarsu a fannonin tattalin aziki da cinikayya, da kara yin mu'amala a tsakanin jam'iyyun kasashen biyu don inganta dangantakar dake tsakanin jam'iyyun biyu zuwa wani sabon matsayi. Kana ya ce, a wadannan shekaru da suka gabata, an fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin ciniki, zuba jari, gine-gine, ayyukan more rayuwa, aikin gona, hakar ma'adinai da dai sauransu. Haka zalika kuma mu'amalar al'adu a tsakaninsu ta kara sada zumunta a tsakanin jama'arsu.

A nasa bangare, Scott ya bayyana cewa, hanyar jirin kasa a tsakanin Tanzania da Zambia da kasar Sin ta taimakawa wajen ginawa sun bude kofar zuwa arewacin kasar Zambia, wadda ta bada taimako sosai ga Zambia. A cikin shekaru biyu da jam'iyyar PF ke kan karagar mulkin kasar, shugabannin kasashen biyu sun sha tuntubar juna, kana an yi hadin gwiwa a fannoni daban daban. A yayin cikon shekaru 50 da kasar Zambia ta samu 'yancin kanta da kuma kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Zambia da Sin, ziyarar mataimakin shugaban kasar Sin za ta kara inganta dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China