Bisa labarin da aka bayar, an ce, ta hanyar amfani da wannan manhaja, jama'ar kasar Zambia za su iya shiga shafukan Intanet na Facebook, da Google, da WikiLeaks da dai sauransu, kana za su iya samun labarai a fannonin kiwon lafiya, da na guraban ayyukan yi, da hasashen yanayi, da kuma na kare hakkin mata kyauta. Sai dai kasancewar Internet.org din na hadin gwiwa ne da kamfanin sadarwa na Airtel na kasar Zambia shi kadai, ya sa masu shiga tsarin Airtel a kasar Zambia kawai ne za su iya samun wannan hidima. (Zainab)