Yanzu akwai kiraye-kiraye da dama dake fitowa daga cikin jam'iyyar MMD dake bukatar tsohon shugaban kasar ya dawo fagen siyasa da fatan ganin halartarsa a zabubukan shekarar 2016 a matsayin dan takarar jam'iyyar.
Wasu bangarorin da suka balle daga tsofuwar jam'iyyar mai mulki, da ta fadi a zabubukan shekarar 2011 bayan shekararu ashirin tana mulkin kasar Zambiya, sun zargi shugaban jam'iyyar na yanzu Nevers Mumba da kasancewa mugun shugaba kuma wanda ya kashe jam'iyyar bayan jerin rashin nasarorin da ta samu a zabubukan 'yan majalisa.
Tsohon shugaban Zambiya ya shaida wa 'yan jarida a birnin Chipata inda aka haife shi dake gabashin kasar Zambiya cewa a shirye yake na dawowa fagen siyasa idan 'yan kasar Zambiya na bukatar haka din.
Ya bayyana cewa zaben dan takarar jam'iyya da zai tsaya a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 ba zai yiwu ba sai idan an samu yin shawarwari tare da shugaban jam'iyyar na yanzu.
Mista Banda, mai shekaru 77 da haifuwa, ya janye daga fagen siyasa bayan da ya fadi a zaben shekarar 2011. (Maman Ada)