A yayin ganawar, Zhang Dejiang ya bayyana cewa, shekarar bana ita ce cikon shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Tanzania, kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Tanzania don cimma moriyar juna da kuma neman ci gaba tare, haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola.
A nasa bangaren, shugaba Kikwete ya ce, kasarsa na son ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, ta yadda zai amfanawa al'ummomin kasashen biyu yadda ya kamata. Bugu da kari, majalisar dokokin kasar Tanzania na son yin hadin gwiwa tare da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin don kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)