Shugaba Jakaya Kikwete ya nuna cewa, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasarsa na da muhimmancin gaske cikin harkokin wajen kasar Tanzania. Duba da cewa kasar Sin ta shafe tsahon lokaci tana baiwa kasar Tanzania goyon baya da tallafi, wanda hakan ya ba da babban taimako ga ci gaban tattalin arziki, da zaman takewar al'ummar kasar.
Cikin wadannan manyan ayyuka, akwai titin-dogo na kasar ta Tanzania zuwa Zambia, lamarin da ya bayyana dankon zumuncin gargajiyar Sin da Tanzania, baya ga cibiyar taron duniya ta Nyerere da Tanzania ta gina, tare da taimakon kasar Sin, wannan ma na nuni ga kyakkyawan hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu a halin yanzu. Hakan kuma ya sa kasashen biyu suke ci gaba da kasancewa abokan arzikin juna na dindindin.
Zhai Jun ya bayyana cewa, kasar Tanzania ita ce muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar kasar Sin a nahiyar Afirka, shi ya sa, Sin ke son ci gaba da karfafa zumunci, da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu tare da Tanzania, ta yadda dangantakar da ke tsakaninsu za ta iya zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka. (Maryam)