Bisa labarin da jaridar "The East Afican" ta kasar Ruwanda ta bayar, an ce daga ranar Litinin din farkon makon nan, kasashen Kenya da Tanzania za su sanya haraji kan shinkafa, da masara, da sukari, da taba, da mai da sauran wasu kayayyaki da ake shigar da su kasar, bisa tsarin yankin biyan haraji rubi daya na kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afirka, ko EAC a takaice.
Wannan mataki dai ya shaida cewa, kasar ta Tanzania ta shiga tsarin yankin biyan haraji rubi daya na EAC, wanda kasashen Kenya, da Uganda da Ruwanda ke bi.
Ya zuwa yanzu, cikin kasashe mambobi 5 na kungiyar ta EAC, kasar Burundi ce kadai ba ta shiga wannan tsari ba, koda yake Burundin ta bayyana cewa tana shirin shiga tsarin a wata mai zuwa. (Zainab)