Ran 9 ga watan Disambar shekarar 1961, kasar Sin ta kulla dangantakar diflomasiya da bangaren Tanganyika, yayin da ta kuma kulla dangantakar diflomasiya da Zanzibar ran 1 ga watan Disambar shekarar 1963. Kana bayan hadewar yankin Tanganyika da na Zanzibar a ranar 26 ga watan Afrilun shekarar 1964, Sin ta mai da wannan rana, ranar kafuwar dangantakar diflomasiya tare da kasar Tanzania.
Bugu da kari dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da bunkasa a tsahon lokaci, har aka kai ga mataki mai gamsarwa a fannoni daban daban da suka hada da tattalin arziki, da cinikayya, da musayar al'adu, ba da ilimi, kiwon lafiya da dai sauransu.
Hakan ya sa, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta zama abokiyar cinikayya mai muhimmanci ta kasar Tanzania, da kuma kasa ta biyu ce a jerin kasashen da suka fi zuba jari a Tanzania. Kuma yawan cinikayya dake tsakanin kasashen biyu a shekarar 2012 ya kai dallar Amurka biliyan 2.47, adadin ya karu ne da kashi 15.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2011. (Maryam)