Yayin da Khalili Muda, mai gabatar da kara na gwamantin kasar ke karanta takardar tuhuma, ya ce, wadannan 'yan ta'adda sun taba kokarin kashe mutane ta hanyar kai hare-haren boma-bomai, bugu da kari, sun dauki mutane daga wurare daban daban a kasar don shigar da su cikin kungiyar ta'addanci ta al-Shabab daga shekarar 2010 zuwa watan Fabrairu na shekarar bana.
Wani jami'in hukumar binciken laifuffuka ta kasar Tanzania ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana ci gaba da neman sauran 'yan ta'addan da suke da hannu a boma-bomai da suka fashe a birnin Arusha . (Maryam)