Yayin shawarwarin, shugaba Jakaya Kikwete ya nuna cewa, shugaba Xi Jinping ya zabi Tanzania da ta zama zangon farko na ziyarar aikinsa a nahiyar Afirka a karo na farko, lamarin ya nuna cewa, ya kasance zumunci mai zurfi tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, Tanzania ita ce abokiyar arzikin Sin a ko da yaushe, Sin na son dukufa tare da Tanzania wajen gina da kuma bunkasa dangantakar abokantakar hadin gwiwa bisa fannoni daban daban don cimma moriyar juna, ta yadda za a iya bunkasa dangantakar tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin sa hannu kan takardun hadin gwiwa na fannoni daban daban da suka shafi cinikayya, zuba jari, gine-ginen kayayyakin more rayuwa, al'adu da dai sauransu. (Maryam)