in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya taya murna ga zababben shugaban kasar Sin Xi Jinping
2013-03-15 11:16:54 cri

A ranar 14 ga wata da dare, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya buga waya ga zababben shugaban kasar Sin Xi Jinping don taya shi murna da hawa karagar mulkin kasar, inda kuma shugabannin biyu suka jaddada bukatar girmama juna tare da fadada hadin gwiwa tsakaninsu.

Obama ya ce, yanzu, an samu wata dama mai ma'anar tarihi wajen tabbatar da makomar dangantakar da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin, kuma Amurka tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, don kafa sabuwar dangantakar da ke tsakanin manyan kasashe tare da Sin cikin armashi, sannan kuma, Amurka tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin, don tabbatar da tsaro, zaman karko, da wadata a yankunan Asiya da tekun Fasific.

A nasa bangare, Shugaban Xi ya bayyana godiya ga Obama kan taya shi murna, sannan ya ce, kasashen Sin da Amurka na da babbar moriya kuma da wasu banbanci a tsakaninsu. Don haka, Sin za ta ci gaba da kiyaye tare da sa kaimi ga raya dangantakar kasashen biyu. Haka kuma, Mr. Xi ya kara da cewa, wajibi ne bangarorin biyu su nace ga yin shawarwari cikin daidaito da tuntubawar juna, da hana sanya siyasa kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya, don tabbatar da dangantakar tattalin arziki da cinikayya ta kasashen biyu domin samun moriyar juna da cimma nasara tare, kuma wannan zai yi amfani ga jama'ar kasashen biyu, da kawo alfanu ga raya tattalin arzikin duniya. Har ila yau, shugaban Sin Mr. Xi ya jaddada cewa, idan aka girmama juna da ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kasashen Sin da Amurka za su samu ci gaba a yankunan Asiya da tekun Fasific.

A lokacin zantawarsu ta wayar tarho, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi game da batun zirin Koriya da tsaron Internet, inda Mr. Xi ya bayyana matsayin da Sin ke tsaye a kai.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China