in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta musunta tanade-tanaden da ke cikin rahoton majalisar dokokin Amurka dangane da kasar Sin a shekarar 2014
2014-10-10 20:57:41 cri

Kwanan baya, kwamitin majalisar dokokin kasar Amurka mai kula da harkokin kasar Sin ya ba da rahoton shekara-shekara kan kasar Sin, inda ya yi suka kan yadda kasar Sin take kiyaye hakkokin dan Adam da kuma gudanar da shari'a a shekarar 2014, tare da mai da hankali kan batun yin gyare-gyare kan harkokin siyasa na yankin Hong Kong na kasar Sin.

Dangane da lamarin, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Jumma'a 10 ga wata a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, rahoton ya yi karin gishiri ga hakikanin abubuwa, inda ya kalli harkokin cikin gida na kasar Sin bisa ga tunaninsa, don haka kasar Sin ta ki amincewa da shi, ta kuma kalubalanci kwamitin da ya daina yin abin da ya kan lalata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka.

Har wa yau Hong Lei ya jaddada cewa, Hong Kong, yankin musamman ne na kasar Sin. Harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda ko wace gwamnati ko hukuma ko ko wani mutum ba shi da ikon tsoma baki cikinsu ta ko wace hanya, ya kamata a yi taka-tsan-tsan, kuma bai kamata a goyi bayan aikace-aikacen da suka saba wa doka ba, sa'an nan kada a nuna misalin da bai dace ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China