A cikin rahoton mai taken "makomar samar da amfanin gona da hatsi" da FAO ta gabatar a cibiyar kungiyar dake birnin Rome, an nuna cewa, dalilin yawan hatsin da ake da shi yanzu, ya taimaka wajen raguwar farashin abinci a duniya.
Sai dai rahoton ya yi kashedi cewa, afkuwar rikice-rikice, gaza samun cikakkun amfanin gona da kuma farashin hatsi mai tsada a cikin gida, akwai kimanin kasashe 33 a duniya ciki har da kasashen Afrika 26 da suke bukatar taimako daga kasashen waje, musamman ma kasashen Afirka ta Tsakiya, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria da kuma Iraki. (Zainab)