Shugaban babban taron MDD karo na 68 John Ashe ne ya sanar da sakamakon zaben, tare da taya Mr. Kutesa murnar zaben nasa.
Tuni dai Kutesa ya bayyana shirin aikinsa a matakin farko, inda ya bayyana cewa, zai ci gaba da inganta manufar ci gaba bayan shekarar 2015, tare da sanya "shirin gudanar da manufofin neman ci gaba bayan shekarar 2015" a matsayin taken babban taron MDDr a karo na 69.
A nasa bangare babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, wanda ya halarci taron na ranar Laraba, ya yi wa Mr. Kutesa fatan alheri, tare da bayyana shi a matsayin gogagge a fannoni daban daban. Har ila yau Mr. Ban ya yi fatan babban taron MDDr zai samu nasara mai gamsarwa, game da cimma burin kawar da talauci na shekarar 2000, da kuma kudurorin neman ci gaba bayan shekarar 2015, a karkashin jagorancin Mr. Kutesa.
Bugu da kari, Mr. Ban ya jaddada cewa, taron koli game da sauyin yanayi da za a kira a watan Satumba a hedkwatar MDD, zai kasance babbar dama ta neman cimma nasarar shawarwari game da batun na sauyin yanayi. Ya kuma ce za a gudanar da taron koli a yayin taron da za a yi daga watan Satumba zuwa na Disamba a yayin babban taron MDDr karo na 69. (Maryam)