in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto ya tabbatar da bunkasuwar rukunin masu karamin karfi a Afrika
2014-08-22 10:51:48 cri

Nahiyar Afrika ta samu muhimmin cigaba a rukunin masu karamin kudin shiga tun yau da kusan shekaru 14, a cewar wani rahoton da aka fitar a ranar Talata a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu.

Akwai iyalai miliyan 15 masu karamin kudin shiga a cikin manyan kasashe 11 dake kudu da hamadar Sahara a wannan shekara, bisa ga miliyan 4,6 a shekarar 2000 da kuma miliyan 2,4 a shekarar 1990, wanda tattalin arzikinsu ya karu da kashi 203 cikin 100 bisa tsawon shekaru 14, in ji wannan rahoto mai taken "Understanding Africa's middle class" da bankin Standard Bank na kasar Afrika ta Kudu ya fitar.

Sai dai, bisa jimillar adadin na iyalai na wadannan manyan tattalin arziki goma sha daya da aka mai da hankalin kansu, kashi 86 cikin 100 ya tsaya a cikin ma'aunin masu kudin shiga mafi kankanta, da nuna kwarewar sabbin kasuwannin nahiyar, in ji rahoton.

GDP na wadannan manyan tattalin arziki goma sha daya da aka yi nazari kan su ya karu da kashi goma tun daga shekarar 2000, a cewar wannan bincike dake amfani da dabarun da ake yawan amfani da su a Afrika ta Kudu.

Bisa tushen amfani da alkaluma na matsayin zaman rayuwa (LSM), rahoton ya ba da alkaluman da za su taimakawa masu zuba jari daukar niyyar wajen zuba jarinsu a nahiyar Afrika.

Wadannan kasashe goma sha daya da aka yi bincike kan tattalin arzikinsu sun hada Angola, Habasha, Ghana, Kenya, Mozambique, Nijeriya, Sudan, Sudan ta Kudu, Tanzaniya, Uganda da Zambiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China