Ranar 29 ga wata, John Kirby, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka ya tabbatar da cewa, yawan kudin da rundunar sojan kasar ta kashe domin daukar matakin soja a kasar Iraki a kwanan baya ya wuce dalar Amurka miliyan 500. Ya yi bayani da cewa, yanzu yawan kudin bai wuce yadda aka zato ba, amma ya kara da cewa, idan nan gaba rundunar kasar za ta sake daukar irin wannan babban matakin soja a ketare, to, ana bukatar kara lisafin kudi na daukar matakin soja na gaggawa a ketare.
A sa'i daya kuma, John Kirby ya ce, a ranar 28 ga wata, a hukumance shugaba Barack Obama na kasar ya bukaci ma'aikatar tsaron kasar da ta gabatar da wani shirin daukar matakin soja a kasar Sham. Yanzu ana tattaunawa kan abubuwan da ke cikin shirin. (Tasallah)