in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya yi kira ga sabon  firaministan kasar Iraq mai jiran gado da ya kafa  gwamnati da za ta kunshi dukkannin kabilun kasar
2014-08-12 15:10:54 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya shawarci sabon firaministan kasar Iraqi mai jiran gado, Haider al-Abadi da ya nada jami'an gwamnati wadanda za su wakilci dukkannin jama'a da bangarorin kasar, ba tare da bata wani lokaci ba.

Shugaban kasar ta Amurka wanda ya ba da wannan shawara daga garin Massachusetts, inda yake yin hutu, ya ce tun farko, shi da mataimakinsa Joe Biden, sun yi magana ta wayar tarho da Dr. Abadi, inda suka taya shi murnar zaman firaministan kasar ta Iraqi, tare da yi masa nuni da cewar, Amurka na goyon bayansa.

Barack Obama ya kara da cewar, zabar Dr. Abadi a matsayin firaministan kasar da shugaban kasar Iraqi Fuad Masoum ya yi wani babban mataki ne na kafa gwamnati da za ta hada kawunan wakilan kabilu dabam dabam na al'ummar kasar Iraki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China