Ministan ilimi a Najeriya Ibrahim Shekarau, ya sanar da dage lokacin komawar 'yan makarantun firamare da na sakandare a dukkanin fadin kasar, a matsayin daya daga matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar Ebola a kasar.
Malam Shekarau ya kara da cewa, an dage komawar 'yan makarantar ne ya zuwa ranar 13 ga watan Oktoba mai zuwa, duk da cewa a baya akan bude makarantun ne a mako na biyu na watan Satumba.
Ministan ilimin Najeriyar ya kuma bukaci hukumomin ilimi na daukacin jihohin kasar, da su aike da ma'aikatansu da suka samu horo game da jinya a makaratu daban daban domin tinkarar halin ko ta kwana. Kaza lika ministan ya umurci dukkanin makarantun da wannan lamari ya shafa da su kammala aikin horar da malamai, da sauran ma'aikatan su kafin ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa, game da matakan da ya dace a dauka kan lokaci. (Amina)