in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Nijar da Togo sun isa Cotonou domin kaddamar da aikin gina hanyar jirgin kasa
2014-04-08 10:37:37 cri

Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya tarbi a ranar Talata a birnin Cotonou takwarorinsa na kasar Nijar Mahamadou Issouffou da na kasar Togo Faure Gnassingbe domin kaddamar da aikin shiyyar na hanyar jirgin kasa, da ake kira "hadewar hanyar jirgin kasa" da za ta hada manyan biranen shiyyar, a cewar wata majiya mai tushe.

Za'a kaddamar da aikin a birnin Cotonou, a cikin wata tashar tsohuwar kungiyar hadin gwiwar Benin da Nijar kan hanyar jirgin kasa (OCBN), wani kamfanin da kasashen biyu ke gudanarwa. Hanyar jirgin kasar za ta hada Lome, Cotonou, Niamey, Ouagadougou da Abidjan.

Babban aiki ne na shiyyar na farfado da aikin OCBN. Shirin da aka dauka a matsayin na dunkulewar shiyyar, tuni an kaddamar da irinsa a birnin Niamey na kasar Nijar, sannan kuma za'a mika kulawarsa ga wani kamfanin hadin gwiwar kasashen da abin ya shafa, tare da jarin Sefa biliyan 7, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 14.

A cewar majiyoyi masu tushe, hukumomin kasar Benin sun dauki niyyar shirya wani babban bikin kaddamarwa a Cotonou a ranar Talata da safe, inda za'a gayyato al'ummar kasar da manyan baki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China