Shugaban kasar Benin Boni Yayi da takwaransa na kasar Nijar Issoufou Mahamadou sun kaddamar a ranar Talata a birnin Cotonou da bikin ayyukan farfado gina da cin gajiyar layin dogo da zai hada Cotonou da Niamey, mai tsawon kilomita 1050.
Wadannan ayyuka suna cikin babban shirin gina hanyar jirgin kasa da za ta hada manyan biranen yammacin Afrika biyar, aikin da ya kasance wani yunkurin dunkulewar tattalin arzikin wannan shiyya ta hanyar farfado hanyar jirgin kasa na kungiyar hadin gwiwar Benin da Nijar ta layin dogo (OCBN), kuma za ta hada biranen Cotonou da Lome, sannan Cotonou zuwa Niamey, har zuwa Ouagadougou da Abidjan.
A cewar shugaban kasar Benin, wannan wani sabon yunkuri na hanyar layin dogo da zai kawo sauki kan dangantakar tattalin arziki tsakanin Benin, Nijar, Burkina Faso, Cote d'Ivoire da Togo. (Maman Ada)