in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kaddamar da layin dogo na Nile da zai hada Khartoum da Atbara
2014-01-21 11:00:18 cri

Gwamnatin kasar Sudan ta kaddamar a ranar Litinin da Layin dogo na Nile da zai hada Khartoum, babban birnin kasar da garin Atbara mai tarazarar kusan kilomita 310 daga arewacin babban birnin kasar.

Mataimakin shugaban kasar Sudan Ibrahim Ghandour, ministan sufurin kasar Ahmed Babikir Nahar, jakadan kasar Sin dake birnin Khartoum mista Luo Xiaoguang, da jami'an diplomasiyyar kasashen waje dake kasar Sudan sun halarci bikin na kaddamar da wannan layin dogo.

A lokacin da yake jawabinsa yayin bikin, mista Ghandour ya bayyana cewa, layin dogo na Nile wani muhimmun shiri ne domin bunkasa layin dogo a kasar ta hanyar kamfanin layin dogo na kasar Sudan, tare da nuna yabo kan dangantakar ta dogon lokaci dake tsakanin Sudan da kasar Sin.

A nasa bangare, ministan sufurin kasar Sudan Ahmed Babikir Nahar ya nuna cewa, wannan shirin layin dogo na Nile ya shafi samar da jirgin kasa guda biyu da za su rika shawagi tsakanin Khartoum da Atabara, da za su rika gudun kimanin kilomita 80 duk awa, ya jaddada cewa, jirgin kasar zai rika tashi su biyu a kowace rana.

Babban aiki shi ne na zamanintar da bangaren sufurin layin dogo a cikin kasar da aka fara tun cikin shekarar 2012 a lokacin da wani kamfanin zuba jari na kasar Sin ya kafa kamfaninsa a birnin Khartoum domin samar da sandunan karafen kankare.

Kasar Sudan dai na fatan zamanintar da kilomita 2000 zuwa 3000 na layin dogon kasar nan da karshen shekarar 2014. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China