Gamayyar kasashen gabashin nahiyar Afrika (EAC) na nazarin wani sabon shirin layin dogo na tsawon kilomita 5000 bisa shekaru 10, in ji wani jami'in kungiyar. Babban darektan EAC kan ayyukan gine-gine Peter Wambugu ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, akwai wani sabon shirin layin dogo da zai kara taimakawa wajen hada kasashe mambobi biyar na wannan kungiya. Kuma aiki ne da zai bukaci dalar Amurka biliyan 10 da zai fito daga gwamnatocin kasashen wannan shiyya, bankin cigaban Afrika, bankin duniya, kasar Sin da kuma tarayyar Turai, in ji mista Wambugu a yayin wani dandalin EAC a Nairobi, babban birnin Kenya.
Taron na kwanaki biyu ya tattara wakilai fiye 200 inda suka mai da hankali kan cigaban dunkulewar shiyyar.
Kungiyar kasashen gabashin nahiyar Afrika ta kunshi kasashen Kenya, Uganda, Tanzania, Ruwanda da Burundi. Gamayyar EAC tana da layin dogo kasa da tsawon kilomita 5000 a halin yanzu. (Maman Ada)