Bayan da aka kaddamar da layin a ran 30 ga watan Yuni na shekarar ta 2011, wannan hanyar dogo ta tabbatar da ingancinta sau da dama, kuma ko da yake saurin jiragen kasa da suke tafiya kan hanyar ya kai kilomita dari uku a kowace sa'a, amma suna tafiya kan hanyar ba tare da wata tangarda ba. Tsarin sadarwa, alamu, wutar lantarki da tsarin samar da wutar lantarki na ciyar da jiragen kasa gaba suna aiki kamar yadda ake fata.
Bayan da aka kaddamar da wannan hanyar dogo mai saurin tafiya a tsakanin biranen Beijing da Shanghai, a bayyane ne an rage tsawon lokacin da aka dauka a tsakanin birane daban daban wadanda suke kusa da hanyar. (Sanusi Chen)