Mataimakin babban manajan kamfanin layin dogon kasar Sin Hu Yadong ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, Mr. Hu yace cikin kilomita 100,000n da ake da shi a yanzu, akwai layin dogo da ya haura kilomita 10,000, da aka gina domin jiragen kasa masu saurin gaske.
Yayin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, gaba daya tsayin layin dogo da kasar ke da shi, bai kai kilomita 22,000 ba, kuma rabinsu ma ba sa aiki a lokacin.
Bisa tsarin gwamnatin kasar ta Sin na yanzu, ana ci gaba da habaka layin dogo, bisa burin tsawaita layin dogon jiragen kasa masu matukar sauri ya zuwa kilomita 19,000 nan da shekarar 2015 mai zuwa. (Bello Wang)