in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya kaddamar da aikin shimfida layin dogo na zamani a Nijeriya
2013-07-05 10:23:45 cri

Kamfanin gine-gine na kasar Sin CCECC a ranar Alhamis din nan ya kaddamar da shimfida layin dogon na zamani a hukumance tsakanin Abuja da Kaduna, abin da ke nuna alamun cewa, za'a kammala aikin cikin lokaci.

Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Namadi Sambo wanda shi ne ya kaddamar da wannan layin dogo a unguwar Idu dake Abuja, babban birnin tarayyar kasar, inda a nan ne tashar ta fara, a cikin bayaninsa ya ce, wannan aikin da za'a yi yana daya daga cikin ayyukan gyaran kasar da kawo cigaba da gwamnatin Nijeriya ta yi alkawari ma al'ummarta na ganin ta farfado da sufuri da zirga-zirga na jiragen kasa kamar a da can baya.

Alhaji Namadi Sambo ya yaba kwarai ga kokarin ma'aikatan kamfanin CCECC, wadanda daga kasar waje suka zo Nijeriya suna aiki ba dare ba rana don ba da nasu gudummuwa don ganin wannan layin dogo ya kammala a cikin lokaci wanda zai zama daya daga cikin ayyukan cigaba na gwamnati. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China