Shugaban reshen fadakarwa na kwamitin, Mao Qun'an ya bayyana cewa, a kokarin nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen shawo kan cutar Ebola, kwamitin, ma'aikatar masana'antukasuwanci, ma'aikatar harkokin waje da hukumar zirga-zirgar jiragengin saman fasinja ta Sin sun hada kayayyakin kiwon lafiya cikin gaggawa, tare da sayen kayayyakin kiwon lafiya ga rukunonin likitancin Sin dake Afirka. Masanan kiwon lafiya daga cibiyar shawo kan cututtuka ta Sin da sauransu sun kafa rukunin masanan zuwa kasashen Afirka, domin ba da taimako wajen shawo kan cutar.
Darektan cibiyar shawo kan cututtuka ta Sin Wang Yu ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da Sin za ta ba da taimako ga kasashen waje ta hanyar tura rukunin masanan kiwon lafiya. Kowane rukuni na kunshe da masana uku a fannin ilmin cututtuka dake iya yaduwa da na kashe kwayoyin cuta.(Fatima)