in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afirka za su iya koyi da fasahohin Sin domin tinkarar Ebola, in ji jami'in WHO
2014-08-09 15:56:40 cri
Mataimakin babban darektan hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa, mista Keiji Fukuda, ya bayyana a Jumma'a 8 ga wata cewa, kasashen yammacin Afirka za su iya koyi da fasahohin kasar Sin wajen tinkarar murar tsuntsaye mai nau'in H7N9 da sauran annoba, sa'an nan ya yi kira da su kara zuba kudi a fannin kiwon lafiyar jama'a, ta yadda za a samu damar shawo kan annobar Ebola da ake fama da ita da kuma take cigaba da janyo hankalin jama'ar kasashe daban daban.

A cewar mista Fukuda, a kokarin tinkarar tarin fuka na SARS da murar tsuntsaye na H7N9, gwamnatin kasar Sin ta zuba makudan kudi a fannin kiwon lafiyar jama'a, abin da ya sa ta samu ci gaba ta fuskar sa ido kan yaduwar cuta, da fahimtar cutar, ta yadda za'a samu damar mayar da martani cikin sauri kamar yadda kasar Sin ta yi yayin barkewar annobar murar tsuntsaye, tare da shawo kanta yadda ya kamata. A cewar Fukuda, wannan wata dama ce ta sa'a samar da irin wadannan fasahohi ga sauran kasashe su koya.

Dangane da yadda kasar Sin ta kai kayayyakin agaji da darajarsu ta kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 30 ga kasashen dake fama da annobar Ebola, Fukuda ya ce kasar Sin ta amsa kiran da hukumar WHO ta yi na kai agaji ga kasashen da annobar ta rutsa da su, kuma tallafin da ta samar yana da muhimmanci ga aikin tinkarar barkewar cutar Ebola.

A nata bangare, hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin, ta fitar da wata sanarwa a ranar 8 ga wata, don kayyade matakan da za a dauka a ofisoshin kwastam domin magance shigowar cutar Ebola a kasar Sin.

Sanarwar ta bukaci a tura kwararrun ma'aikata masu fasahar tinkarar cuta mai yaduwa zuwa ofisoshin kwastam daban daban, da kuma kokarin horar da sauran ma'aikatan kwastam, da aiwatar da atisaye, ta yadda za su samu damar kwarewa kan binciken alamun cutar da shawo kanta yadda ya kamata.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China