in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Iran da Amurka sun gudanar da wata tattaunawa a kan makamashin nukiliya a Geneva
2014-08-08 11:00:00 cri
Kawo yanzu, babu bayanai filla filla da aka ba da game da taron da aka yi jiya Alhamis tsakanin Amurka da Iran a kan maganar makamashin nukiliya a Geneva.

Kamar yadda hukumomin Amurka suka bayyana, masu tattaunawa daga kasar Amurka sun kunshi Bill Burns, mataimakin sakataren harkokin waje da Wendy Sherman, mai ba da taimako ga sakataren harkokin wajen kasar, kuma sun gana da jami'an kasar Iran domin ci gaba da tattaunawa a kan makamashin nukiliya.

Kafofin watsa labarai na Iran sun bayyana cewa, mataimakin ministan harkokin waje na Iran Majid Takht-e Ravanchi da Abbas Araqchi su ne suka jagoranci bangaren kasar Iran wajen tattaunawar da kuma kwararru daga kasashen biyu su ma suna cikin jerin wadanda suka shiga cikin taron a kan makamashin nukiliya.

Amurka da abokanan huldar ta na zargin Iran da samar da makamashin nukiliya, to amma kasar ta Iran ta ce ita shirinta na nukiliya na amfanin kanta ne ba na makamai ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China