Kasar Amurka ta sanar da zuba dalar Amurka biliyan 33 zuwa nahiyar Afrika a rana ta biyu ta dandalin Amurka da Afrika dake manufar karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya da Afrika, in ji fadar White House a ranar Talata.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanar da wani sabon zuba-jari na dalar Amurka biliyan 7 domin bunkasa fitar da kayayyaki da zuba jarin Amurka a Afrika bisa tsarin kamfen "Doing Business in Africa" (DBIA), a albarkacin dandalin Amurka da Afrika da ya gudana a yayin wannan dandali, a cewar sanarwar White House.
Haka su ma kamfanonin Amurka sun bayyana sabbin kwangiloli da suka shafi fannonin makamashi mai tsabta, jiragen sama, bankuna da gine-gine bisa jimillar dalar Amurka fiye da biliyan 14. Bisa kaddamarwar shugaba Obama a shekarar 2013, shirin "Power Africa" na da manufar rubunya samar da wutar lantarki a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, haka kuma an samu karin zuba-jari na dalar Amurka biliyan 12 daga bangaren masu zaman kansu, bankin duniya da kuma gwamnatin Sweden.
Haka kuma Obama ya kafa a ranar Talata wani kwamitin tuntubar juna na fadar shugaban kasa kan kamfen DBIA domin kara ba da kwarin gwiwa ga kamfanonin Amurka domin bude harkokinsu da zuba jari a nahiyar Afrika. Kwamitin yana kunshe da mambobi 15 da suka fito daga bangaren masu zaman kansu, har da kananan kamfanoni.
Kimanin shugabanni 50 na gwamnatocin Afrika suna halartar wannan dandali na kwanaki uku da aka bude a ranar Litinin a birnin Washington. (Maman Ada)