Mr. Wang ya ce, kudurin na da muhimmiyar ma'ana wajen cimma fatanmu wajen warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar siyasa, kasar Sin tana fatan kasashen shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da kuma kasar Iran za su iya yin amfani da wannan dama yadda ya kamata don kulla wata yarjejeniya mai dorewa daga dukkan fannoni wadda za ta iya kwantar da hankulan gamayyar kasa da kasa da na kasar Iran.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta ba da babbar gudumawa tun lokacin da aka fara taron shawarwari kan kulla yajejeniya, don ciyar da yunkurin kulla yarjejeniyar daga dukkan fannoni gaba.
Daga bisani kuma, fadar White House ta kasar Amurka ta ba da wata sanarwa, inda ta nuna cewa, ko da ana cin karo da bambancin ra'ayoyi tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa dangane da yajejeniyar, amma dukkansu suna dauke da kyayyawan fata kan cimma wannan yarjejeniyar. (Maryam)