Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka da cutar ta shafa taimakon jin kai na gaggawa domin yakar cutar Ebola.
Yanzu haka dai wannan cuta ta Ebola na ci gaba da yaduwar a wasu daga kasashen dake yammacin nahiyar Afirka, musamman ma a kasashen Guinea, da Liberia da kuma Saliyo.
An bayyana cewa tawagogin ma'aikatan jinya da kasar Sin ta tura kasashen da ake fama da wannan annoba na ci gaba da gudanar da ayyukansu. A sa'i daya kuma kasar Sin za ta ci gaba da samar da kayayyakin agaji don ba da taimako gare su yadda ya kamata wajen yaki da cutar ta Ebola. (Maryam)