Hukumar kare barkewar cututtuka masu hadari ta kasar Sin ta umarci jami'an kwastam da su kara azama wajen tantance mutanen dake shiga kasar don gudun bullar cutar Ebola.
Mahukuntan sashen lura da kayayyakin da ake shigarwa kasar na hukumar sun bayyana cewa, za su matsa kaimi wajen binciken fasinjoji, da kayayyaki, da ma wasu nau'o'in abinci masu nasaba da dabbobin dake shiga kasar ta jiragen sama, daga kasashen da aka samu bullar cutar ta Ebola. A hannu guda kuma, za a inganta harkokin tsaftar harkar sufuri da kayayyakin da ke shiga da su kasar.
Bugu da kari hukumar ta ce, za ta maida hankali ga fadakar da al'umma game da illar wannan cuta, da kuma hanyoyin kandagarkin yaduwarta.(Saminu Alhassan)