in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwararsa ta kasar Brazil
2014-07-18 14:43:47 cri

A ranar Alhamis 17 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwararsa ta kasar Brazil Dilma Rousseff a birnin Brasília, inda a lokacin tattaunawar shugabannin biyu suka takaita kyakkyawan sakamakon da suka samu a cikin shekaru 40 da suka wuce tun bayan kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu.

A tattaunawar tasu sun yanke shawara cewa, za su yi amfani da sakamakon da suka samu, sannan za su tsara makomar dangantakar da ke tsakaninsu bisa hangen nesa, baya ga tsaya tsayin daka kan hadin kansu. da mai da hankali kan bunkasuwa, ta yadda za su ciyar da dangantakar abokantaka a tsakaninsu a dukkan fannoni zuwa gaba bisa manyan tsare-tsare.

Shugabannin biyu sun jinjina taron shawarwari karo na 6 a tsakanin shugabannin kasashen BRICS, inda suke ganin cewa, kafuwar bankin raya kasashen na BRICS da kuma asusun ajiye kudaden gaggawa, abu ne dake da wata muhimmiyar ma'ana wajen kyautata tsarin duniya, da sa kaimi ga kafa wani tsarin tattalin arziki da harkokin kudi yadda ya kamata. Kasashen Sin da Brazil za su ci gaba da sa kaimi ga hadin kai a tsakanin kasashen BRICS da sauran kasashe masu tasowa.

Bayan shawarwarinsu, shugabannin biyu sun gabatar da wata sanarwar zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu sannan daga baya suka halarci bikin rufe taron shekara-shekara na 2014 a tsakanin masu masana'antun Sin da Brazil. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China