A cikin jawabinsa wajen taron, shugaba Xi Jinping ya sanar da matakan da kasar Sin ta gabatar wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Latin Amurka da Caribbean. A jawabin nashi mai teken "yi kokarin kafa tsarin bai daya na samun bunkasuwa tare", ya gabatar da shawawari biyar da suka hada da samun fahimtar juna a fannin siyasa, hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya don moriyar juna, koyar da juna a fannin al'adu, inganta hadin kai kan harkokin kasa da kasa, gami da kyautata dangantaka a tsakanin bangarorin biyu, a kokarin kafa tsarin bai daya na samun bunkasuwa tare.
Ita ma shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana godiyarta ga shugaba Xi Jinping da ya gabatar da muhimman shawarwari, kuma ta yi alkawarin cewa, kasashen Latin Amurka da Caribbean za su yi kokari tare da kasar Sin wajen aiwatar da wadannan shawarwarin tare da kafa dandalin tattaunawa don samun bunkasuwa da wadata tare.
Bayan taron, shugabannin kasashen sun gabatar da hadaddiyar sanarwa. (Zainab)