in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci Venezuela ta shiga a dama da ita a harkokin ci gaba da Sin ke samu
2014-07-22 10:04:46 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bukaci mahukuntan kasar Venezuela da su yi hadin gwiwa da Sin domin cin gajiyar irin daukakar da kasar ke samu ta fuskar ci gaba, yana mai fatan kasashen biyu za su yi hadin gwiwa wajen karfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Shugaban na Sin wanda ya bayyana hakan yayin da yake halartar bikin rufe babban taron hadin gwiwar kasashen biyu karo na 13, ya kara da cewa, kasarsa na ci gaba da gudanar da sauye-sauye, da kara bude kofa, da fadada ci gaba ta fuskar bunkasar tattalin arziki, matakan da za su ba da karin dama ta habaka dangantakar kasashen biyu.

Shi kuwa a nasa bangare, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, jinjinawa shugaba Xi ya yi bisa ziyarar da ya gudanar a kasarsa, yana mai bayyana ta a matsayin ziyarar dake cike da nasarori.

Gabanin rufe taron dai, shuwagabannin kasashen biyu sun halarci bikin rattaba hannu kan yarjeniyoyin da suka amince da su, wadanda suka jibanci sashen makamashi, da cinikayya, da samar da ababen more rayuwa. Sauran sassan sun hada da fannin hakar ma'adanai, da sashen noma da kuma na bunkasa sabbin fasahohi.

Shugaba Xi na ziyarar aiki ne a kasar ta Venezuela, kasar da ta kasance ta uku a jerin kasashen Latin Amurka hudu, da aka tsara zai kaiwa ziyara a wannan karo.

Sin dai ta kasance kasa dake matsayi na biyu ga Venezuela, a yawan huldar da ta jibanci cinikayyar mai, da sauran fannonin kasuwanci, kuma Venezuela tana matsayi na hudu a yawan harkokin cinikayya da kasar Sin a tsakanin dukkanin kasashen dake Latin Amurka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China