Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya isa kasar Venezuela domin fara wata ziyarar aiki, kuma tuni shugaban kasar ta Venezuela Nicolas Maduro, ya amshe shi a filin jirgin saman Venezuela.
Wannan ziyara, ita ce ziyara ta zango na uku da shugaba Xi ya kai a kasashe 4 a yankin Latin Amurka.
A yayin jawabinsa bayan ya isa kasar, shugaban kasar na Sin Xi Jinping ya ce, kyakkyawar abokantaka tsakanin Sin da Venezuela wani abu ne da aka dade ana dasawa, kana kuma ya ba da yarjejeniyar aiki tare domin ci gaban kasashen. Xi, ya yi hasashen cewar, kulla hulda dangantaka a nan gaba wani abu ne dake da alamun samun nasara.
A yayin ziyarar, dukanin bangarorin biyu, ana sa rai za su rattaba hannu a kan yarjejeniya aiki tare a bangaren maganar kudi da gina ababen bunkasa rayuwa, da kuma maganar noma da kuma sabbin fasahohi na zamani. (Suwaiba)