in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da manyan shugabannin kasar Argentina
2014-07-20 17:10:06 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da mataimakin shugaban kasar Argentina, kuma shugaban majalisar dattijan kasar Amado Boudou, da shugaban majalisar wakilai Julian Dominguez a ranar Asabar 19 ga watan nan a birnin Buenos Aires.

Yayin ganawar ta su shugaba Xi ya jaddada cewa, hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Argentina, ya dace da halin da ake ciki a yanzu, game da kokarin bunkasa yanayin zaman lafiya da ci gaba, wanda ke haifar da moriya ga al'ummun kasashen biyu.

A cewar shugaban, ya gana da takwaran sa na kasar Madam Cristina Fernandez de Kirchner, inda shuwagabannin biyu suka cimma matsaya game da shawarwarin daga dangantakar dake tsakanin kasashen su zuwa sabon matsayi bisa manyan tsare-tsare.

Har ila yau shuwagabannin sun cimma matsaya, kan karfafa hadin kai, da mu'ammala tsakanin su.

Game da hakan Mr Xi ya ce yanzu haka kasashen biyu na fuskantar zarafin raya dangantakar dake tsakaninsu, don haka ya kamata su mai da kan su kasashe muhimmai ga juna, a fagen samun bunkasuwa yadda ya kamata, da kara hadin gwiwa, da cimma moriyar juna, da sa kaimi ga samun bunkasuwa a dukkanin sassa.

A nasu bangare, Amado Boudou da Julian Dominguez sun bayyana ziyarar da Mr Xi ya yi a wannan karo, a matsayin hanyar karfafa amincewa da juna, da hadin kai tsakanin kasashen biyu, baya ga zai ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba.

Jami'am sun ce Argentina tana goyon bayan manufofin da Sin ke bi, wajen samun bunkasuwa da aka yiwa lakabi da "Mafarkin Sin". Inda suka ce bunkasuwar Sin za ta yi tasiri ga samar da alfanu a sassan duniya.

Kana hadin gwiwa da kasashen biyu suke yi zai yi babban tasiri ga samun bunkasuwar kasashen biyu, baya ga kuma bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashe mafiya karfi a fannin tattalin arziki da kasashe masu tasowa, ta yadda za a kai ga kafa wani tsari na duniya dake cike da adalci da daidaito.

A cewar su hakan ne ma ya sa majalissu da jam'iyyu daban-daban na kasar, ke goyon bayan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, suke kuma fatan kara hadin gwiwa da zurfafa zumunci tsakanin su da kasar Sin a nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China