A yayin shawarwarin, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan manyan batutuwan dake shafar yankunansu. Game da halin da ake ciki a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, Xi Jinping ya nuna damuwa sosai ga lamarin. Kasar Sin ta bayyana matsayinta na bukatar kasashen biyu da a tsagaita bude wuta cikin hanzari, kana ta nuna goyon baya ga MDD da kungiyar kawancen Larabawa da kasashen dake yankin da su yi kokarin shiga-tsakani kan batun. Kana kasar Sin ta nuna goyon baya ga jama'ar kasar Palesdinu, kuma ta ce, yin shawarwari cikin lumana ita ce hanya daya kawai wajen samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, don haka kamata ya yi bangarori daban daban da abin ya shafa su warware matsaloli da cimma ra'ayi daya don maido da yin shawarwari a tsakaninsu tun da wuri. Sai dai kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari wajen ganin an sassauta halin da ake ciki a tsakanin kasashen biyu da kiyaye zaman lafiya a yankin. (Zainab)