Ofishin kula da yawan al'umma na hukumar kula da harkokin tattalin arziki da zaman takewar al'umma ta MDD ne ya bayyana hakan, a yayin taron gabatar da rahoton game da binciken da aka yi kan makomar bunkasuwar biranen kasa da kasa na shekarar 2014 da aka yi a hedkwatarsa dake birnin New York a wannan rana.
Rahoton ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2050, yawan al'ummar duniya zai karu da biliyan 2.5, kuma kashi tara bisa goma daga cikinsu za su kasance a biranen Asiya da Afirka, kana kasashen da za su samu karuwar yawan mutane mafi yawa a nan gaba su ne Indiya, Sin da kuma Najeriya. (Maryam)