Babban yabon da ake iyar baiwa Nelson Mandela bai tsaya ga kalamai ko shirya bubukuwa ba, amma tabbatar da shi ta hanyar kafa wata kyauta domin girmama gudunmuwa da gadon da ya bar ma duniya, in ji babban sakatare na MDD, mista Ban Ki-moon, bayan taron ya cimma wani kudurin kafa wannan kyauta.
Tun farkon matakan da aka dauka har zuwa sanarwar da aka fitar a ranar 18 ga watan Juli a matsayin ranar kasa da kasa ta tunawa da Nelson Mandela, taron MDD ya tsaya kusa da tarihi, tare da mutanen da suka fi son mu, in ji mista Ban, tare da tunatar da cewa Nelson Mandela ya amince da kyautar Nobel ta zaman lafiya, kuma Nelson Mandela ya bayyana cewa yana wakiltar miliyoyin mutane dake ganin cewa idan aka kuntatawa mutum daya kamar an kuntatawa kowa ne.
Bisa kudurin da aka cimma, hanyoyin da za'a bi wajen bada wannan kyauta ta Nelson Mandela za'a fitar da su nan da watanni shida masu zuwa. (Maman Ada)