in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a martaba rawar da sassan da abin ya shafa ke takawa a lokacin da ake aiwatar da ayyukan shimfida zaman lafiya, in ji wakilin Sin
2014-06-12 16:04:12 cri
Jiya Laraba 11 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a hedkwatar majalissar dake birnin New York cewa, ya kamata a martaba rawar da kasar da abin ya shafa ke takawa, a yayin da ake aiwatar da ayyukan shimfida zaman lafiya, da nufin kare fararen hula bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD.

A wannan rana, an kira wani taro na kwamitin sulhu na MDD, game da ayyukan majalisar na kiyaye zaman lafiya. A yayin taron, Mr. Wang ya bayyana cewa, ganin yadda ake jibge sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD, da yawansu ya zarce rabi a nahiyar Afirka, ya kamata MDD da gamayyar kasa da kasa, su karfafa hadin gwiwarsu tare da kungiyoyin nahiyar Afirka kan wannan aiki, su mara wa kungiyar AU da sauran kungiyoyin yankin baya,, su kuma tallafawa Afirka wajen inganta karfinta. Wannan mataki a cewarsa zai baiwa AUn fifiko, da sauran kungiyoyin nahiyar cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Mr. Wang ya kara da cewa, a matsayinta ta kasar da ta fi tura yawan sojojin kiyaye zaman lafiya a cikin kwamitin na tsaron MDD, kasar Sin za ta ci gaba da marawa aikin na MDD baya cikin himma da kwazo, don ba da gudummawarta ga aikin kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China