A gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar MDD dake birnin New York a wannan rana, kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, bisa kididdigar da tawagar MDD mai bada taimako ga Iraki ta yi, an ce, yawan fararen hula da suka mutu a jihohin Ninevehdin, Diyala da kuma Salah ad Din ya kai 757, yayin da mutane 599 suka ji rauni. A birnin Baghdad da kuma yankin kudancin kasar, kuma mutane 318 ne suka mutu a sakamakon hare-hare, kana wasu mutane da dama sun rasu a sakamakon fashewar bom din da aka dasa a cikin mota.
Dujarric ya kara da cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen dake wannan yanki da su yi kokarin tabbatar tsaro da zaman lafiya a kasar Iraki da kuma ta Syria. (Zainab)