in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ci gaba da yin musayar wuta a kasar Iraki
2014-06-20 11:07:44 cri
Sojojin kasar Iraki da dakaru masu adawa sun ci gaba da yin musayar wuta a wurare daban daban na kasar a ranar 19 ga wata.

Kakakin rundunar sojojin kasar Iraki, Qassim Atta ya bayyana a gun taron manema labaru a wannan rana cewa, bisa taimakon jiragen sama na yaki, sojojin tsaron kasar sun cimma nasarar dakile hare haren dakaru masu adawa suka kai wa kamfanin samar da man fetur na birnin Baiji. Kuma a birnin Tal Afar dake arewacin kasar Iraki da dakaru masu adawa suka kwace, sojojin kasar da dakaru masu adawa sun yi musayar wuta, inda sojojin gwamnati suka kashe dakaru 50 tare da lalata motoci 15. A jihar Diyara dake gabashin kasar, sojojin gwamnatin kasar sun kai hari kan sansanin mayakan ta jiragen sama mai saukar ungulu, wanda ya haddasa mutuwar dakaru 15.

Game da wannan sabon rikici na kasar Iraki, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanar a ranar 19 ga wata cewa, za a tura manazartan aikin soja kimanin 300 zuwa kasar Iraki, amma ya jaddada cewa, ba za a tura sojoji zuwa kasar Iraki ko shiga yaki ba. Amma idan har aka kawo illa ga moriyar kasar Amurka, watakila za a dauki matakan soja kamar kai hari ta sama. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China