in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan za a tabbatar da zaman lafiya a Iraki cikin hanzari
2014-06-17 20:46:49 cri
Yau Talata 17 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin madam Hua Chunying ta bayyana cewa, Sin tana mai da hankali sosai kan yanayin da ake ciki a Iraki, kuma tana fatan za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan da nan.

A gun taron, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, yanzu kasar Iraki na tangal tangal, kuma yankin kudu maso gabashin Iraki na da muhimmanci ga wasu kamfanonin man fetur na Sin, ko Sin za ta tura tawaga ko jami'anta zuwa wurin domin fahimtar yanayin da ake ciki?

Madam Hua ta amsa cewa, Sin tana mai da hankali sosai kan yanayin da ake ciki a kasar, kuma tana dora muhimmanci kan tsaro da 'yanci da moriyar jama'ar Sin da kamfanonin Sin a Iraki. Har yanzu ba a bayar da wata sanarwar game da tura tawagar Sin zuwa Iraki ba. Kuma za a dauki kwararan matakai bisa yanayin da za a fuskanta, domin ba da kariya ga tsaron Sinawan da ke kasar Iraki. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China