An ce an harbe wasu fursunoni fiye da 10 dake tsare a wani kurkuku, yayin musayar wuta da aka yi tsakanin bangarorin biyu a jihar Diyala dake gabashin kasar.
A hannu guda kuma gwamnatin kasar ta Iraki ta dora alhakin abin da ke faruwa a kasar kan kasar Saudiyya, wadda ta zarga da samarwa 'yan adawar kudade da goyon baya.
Wata sanarwa daga ofishin firaministan kasar Irakin ta ce alhakin halin zubar da jini, da tashin hankalin dake wakana a kasar na wuyan kasar Saudiyya. Har ila yau sanarwar ta yi gargadi ga gwamnatin Saudiyyar da ta mai da hankali kan batutuwan da suka shafi cikin gidanta, da kuma daina nuna kyama ga mabiya akidar Shi'a dake kasarta. (Zainab)