Wani dan sanda a jihar al-Anbar ya bayyana cewa, an kai hare-hare kan birnin Qaim da na Rutba dake jihar ta sama, hare-haren da suka haddasa mutuwar mutane a kalla 69. A halin yanzu, wadannan biranen biyu suna karkashin ikon dakarun ISIS masu adawa da gwamnati.
A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, kakakin bangaren soja na kasar Iraki Qassim Atta ya musanta labarin dake cewa 'yan adawa suka kwace kamfanin samar da mai na Baiji, wanda shi ne mafi girma a kasar. Atta ya kara da cewa, yanzu haka jami'an tsaron kasar suna rike da ikon wannan kamfani. Kana sojojin gwamnatin kasar sun cimma nasarar fatattakar dakarun ISIS daga harabar kamfanin. (Zainab)