in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
John Kerry ya ce Amurka na duba yiwuwar taimakawa Iraqi a yakin da take yi da masu ta da kayar baya
2014-06-15 16:00:27 cri
Sakataren wajen Amurka John Kerry, ya bayyana shirin kasarsa na taimakawa kasar Iraqi, a yakin da dakarun take yi, da mayakan kungiyar nan ta ISIS dake kokarin mamaye yankunan kasar.

Yayin wata tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Iraqi Hoshyar Zebari, sakataren wajen Amurkan ya jaddada kudurin gwamnatin kasarsa, game da bude hanyoyi daban daban na tallafawa Iraqi, ciki hadda tuntubar makwaftan kasar ta Iraqi game da batun bada nasu taimako, a wannan lokaci da Iraqin ke cikin mawuyacin hali.

Cikin wani jawabin da ya gabatar a ranar Jumma'ar da ta gabata, shugaba Barack Obama ya zayyana sharuddan da suka jibanci tallafin da kasarsa ke iya baiwa Iraqin, ciki hadda bukatar mahukuntan kasar su kokarta wajen kawo karshen rabuwar kawunan al'ummarta.

A kuma jiya Asabar, sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya bada umarnin sauyawa wani babban jirgin ruwan dakon jirage na Amurka wuri, daga tekun Arebiya zuwa yankin Gulf. Matakin dake da alaka da yiwuwar amfani da shi, idan har bukatar baiwa Amurka ko manufofin ta kariya ta bijiro a wannan yanki. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China