in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Iraki sun sanar da samun nasara a yakin da suke yi da dakarun ISIS
2014-06-16 11:00:03 cri
Kakakin ofishin kwamandan sojojin kasar Iraki Qassim Atta, ya sanar da cewa, sojojin Iraki sun samu galaba a yakin da suke yi da dakarun kungiyar ISIS masu tsattauran ra'ayi.

Mr Atta ya bayyana hakan ne a gun wani taron manema labaru da aka yi a ranar 15 ga wata bisa agogon wurin, yana mai cewa cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sojojin kasar Irakin sun harbe dakarun ISIS 279, tare da kwace birane da dama dake arewacin kasar daga ikon kungiyar.

Kaza lika Atta ya kara da cewa, sojojin kasar sun cimma nasarar dakile mamayar da yankunan kasar da dakarun ke kokarin yi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China