An dai gudanar da zaben sabuwar majalissar dokokin kasar ta Iraki ne a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata, inda jam'iyyar "State of Law alliance" ta firaminista Nuri Al-maliki ta samu rinjaye, da kujeru 92 cikin daukacin kujerun wakilci 328.
A daya bangaren kuma babbar kwamishiyar MDD dake kula da harkokin kare hakkin bil Adama Navanethem Pillay ta bayar da wata sanarwa a birnin Geneva, inda ta ce ofishinta ya samu labari cewa, a 'yan kwanaki biyar da suka wuce dakarun kungiyar ISIL sun hallaka sojoji, da 'yan sanda, da sauran ma'aikatan gwamnatin kasar ta Iraqi da suka kame, da yawansu ya haura dari daya.
Pillay ta tabbatar da cewa, za a dauki wadannan ayyuka na kisan kai a matsayin laifukan yaki.
Kasar Iraqi dai ta auka hargitsi ne tun bayan janyewar da sojojin Amurka suka yi daga kasar a shekarar 2011 da ta gabata. (Bilkisu)