Kungiyar AU ta nada kwamitin bincike game da kasar Sudan ta kudu
A ranar jumma'an na 7 ga wata kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta sanar da nada wani kwamiti akan kasar Sudan ta kudu wanda ta dora ma alhakin binciken take hakkin bil adama da sauran ayyukan cin zarafin da aka yi lokacin tashin hankalin da ya gudana a kasar. Shugaban kungiyar Madam Nkosazana Dlamini-Zuma wadda ta sanar da hakan ma manema labarai a cibiyar kungiyar dake Adis ababa babban birnin kasar Habasha,tace kwamitin ya kunshi mambobi 5 daga fannoni daban daban. Madam Zuma tayi bayanin cewa taron kwamitin zaman lafiya da tsaro da aka yi a watan Decembar bara a Banjul babban birnin kasar Gambiya ya bukaci kungiyar ta AU data nada wannan kwamitin bincike. Tsohon shugaban kasar Nigeriya Olusegun Obasanjo ne dai zai jagoranci Kwamitin binciken. (Fatimah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku